Ƙungiyar bunƙasa tttalin arziƙin ƙasar Afrika ta yi Alla-wadai da yunƙurin juyin mulki da aka yi a ƙasar Nijar.

Shugaban ƙungiyar Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana haka a wata sanarwa bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a ƙasara safiuyar yau Laraba.


Shugaban y ace ƙungiyar ba za ta lamunci juyin mulki a ba musamman a lokacin da aka mayar da hankali wajen bunƙasa tattalin arziki.
Sannan ya ce ƙasashen duniya da ke goyon bayan mulkin demokaraɗiyya ba za su lamunci juyin mulki daga sojoji ba kuma ba za su goyi bayan haka ba.
Sannan ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da sa ido domin tabbatar da cigaba da mulkin demokaraɗiyya a ƙasar.
A safiyar ranar Laraba ne dai aka wayi gari sojoji sun rufe ƙofofin shiga ma’aiakatun gwamnati da fadar shugaban ƙasa bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a ƙasar.
Daga cikin wuraren da aka aike da jami’an tsaro har da tashar talabiji ta ƙasar.