Aƙalla sojoji Bakwai ne su ka rasa rayuwarsu yayin da aka hallaka farar hula da dama a wani sabon hari da ƴan bindiga su ka kai jihar Zamfara.

 

Harin ya faru a yammacin ranar Litinin a Kangon Garacce da ke Dangulbi a ƙaramar hukumar Maru ta jihar.

 

Wani mai suna Lawal Ɗangulbi ya shaida cewa jami’an sojin na kan hanyarsu bayan sun samu kira a kan harin da ƴan bindiga su ka kai garin kuma a kan hanyarsu ne su ka buɗe musu wuta.

 

Ya ce ƴan bindigan sun kasa kansu wuri daban-daban yayin da wani rukuni daga ciki su ka shiga garin wasu kuwa su ka tsaya a bayan gari.

 

Sojojin bakwai ne su ka rasa rayuwarsu yayin da aka hallaka farar hulka aƙalla Ashirin a garin.

 

Jihar Zamfara na fama da hare-haren ƴan bindiga tsawon lokaci wanda hakan yay i silar raba mutane da dama da muhallinsu tare da rasa rayuka masu yawa.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: