Gwamnatin Tarayya ta ce daga watan Satumbar wannan shekara za ta fara bai wa dalibai rance.

Mashawarcin Shugaban Kasa kan Ayyuka na Musamman Dele Alake ne ya bayyana haka har ya kara da cewa gwamnati za ta bullo da sabbin hanyoyin tallafa wa dalibai masu karamin karfi.

Daga cikin abubuwan da gwamnatin ta tsara na tabbatar da ganin kowanne dalibi ya kammala karatunsa a kan lokaci, komai karamin karfin iyayensa, akwai daukar su aikin wucin gadi a makarantunsu, bayar da rance da kuma daukar nauyin wadanda suka cancanta a cikinsu, a cewarsa.

Alake ya ce dokar bai wa dalibai rance da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu za ta fara aiki gabanin shiga sabuwar shekarar karatu mai kamawa a watan Satumba.

Sai dai kuma bai ce uffan ba game da matakai ko shirye-shiryen da gwamnatin ta yi domin tabbatar da hakan.

Ya kuma nesanta Gwamnatin Tarayya da karin kudin rajista da sauransu da jami’o’inta suka yi, inda ya ce, har kwanan gobe ba a biyan kudin makaranta a jami’o’in, don haka babu gaskiya a rahoton da wasu kafofin yada labarai suka wallafa cewa gwamnatin ta kara kudin makaranta a jami’o’inta.

Ya bayyana cewa, “Shugaba Tinubu zai ci gaba da yin tsayuwar daka domin cika alkawarinsa na ganin kowane dan Najeriya komai matsayinsa ko karfin iyayensa, ya samu ilimin gaba da sakandare.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: