Rundunar sojin Nijar ta goyi bayan juyin mulkin da sojoji suka sanar a gidan talabijin na ƙasar, inda suka tabbatar da hamɓarar da gwamnatin farar hula ta Shugaba Mohammed Bazoum.

Shugaban dakarun sojin ƙasa na kasar ya ce sun goyi bayan juyin mulkin ne saboda guje wa rikici tsakanin rundunonin tsaron ƙasar.
Goyon bayan na sojoji ga masu juyin mulkin na ƙara tabbatar da juyin mulkin.

Sojan da ya jagoranci juyin mulkin, Kanal Amadu Abdulrahman ya rushe dukkan shugabannin siyasa a fadin Kasar.

Yanzu dai sojoji ne ke riƙe da shugabancin ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da kuma Chadi, sai kuma kasar Sudan da yanzu haka ake rikici a ƙasar tsakanin dakarun soji da dakarun RSF.
Akwai yiyuwar ƙawayen Nijar da suka haɗa da Amurka, su mayar da hankali wajen ganin komai ya daidai ta a ƙasar.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres “ya yi kakkausar suka ga sauyin gwamnati da aka samu a Jamhuriyar Nijar ba bisa ka’ida ba, kamar yadda kakakinsa ya Stephan Dujarric ya bayyana a jiya Laraba.
Hakan na zuwa ne bayan da sojojin Nijar suka sanar da juyin mulki a gidan talabijin na kasar, inda suka ce sun jingine aiki da kundin tsarin mulkin kasar, tare da dakatar da dukkan hukumomi da kuma rufe iyakokin ƙasar.
Mista Guterres ya ce ya damu matuka da tsare Shugaba Mohamed Bazoum kana kuma ya damu da lafiyarsa, in ji kakakinsa Stephane Dujarric a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar tayi kira da a gaggauta kawo karshen duk wasu ayyukan da ke kawo cikas ga tsarin dimokuradiyya a Nijar, da nahiyar Afrika.