Kungiyar kwadago a Najeriya NLC ta ce ba gudu ba ja da baya wajen tafiya yajin aikin da ta tsara a ranar Laraba.

Kungiyar na ci gaba da mayar da hankali wajen hada kan ma’aikata don ganin an tafi yajin aikin nan da kwana biyu masu zuwa.
Matakin hakan ya biyo bayan tashi baram-baram da kungiyar ta yi bayan wani zama da wakilan gwamnatin tarayya a Abuja.

Matsin rayuwa bayan ƙara farashin litar mna fetur na daga dalilai da ya sa kungiyar za ta tafi yajin aikin.

A baya kungiyar ta shirya tafiya yajin aikin sai dai ta janye daga baya bayan sulhu da aka yi da bangaren gwamnatin tarayya.
Daga bisani kotu ta dakatar da kungiyar daga tafiya yajin aikin.
Ma’ajin kungiyar na ƙasa Hakeem Ambali ya shaida yadda gwamnatin ta yi watsi da zama zaman da aka tsara a ranar Juma’a.
A halin yanzu kungiyar na cigaba da samun goyon bayan ma’aikata don tafiya yajin aikin gama gari a ranar Laraba.
Karin albashi da raba tallafi na daga cikin muradun da kungiyar ta saka a zaman da aka yi da farko.