Tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.

Ganduje ya zama shugaban bayan amincewa da shi a majalisar zartarwa da jamiyyar ta yi a yau.
Kafin kasancewarsa shugaban jam’iyyar awanni kaɗan shugabannin jam’iyyar APC na jihohin Najeriya su ka mara masa baya a wata ziyara da su ka kai gidansa a Abuja.

Ya maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu wadan aya ajiye muƙamin a watan da ya gabata.

An zargi Sanata Abdullahi Adamu daa karya dokar jam”iyyar kuma ake zaargin ana gab da tsigeshi, sai dai ya ya ajiye muƙamin kafin saukeshi .
A zaman da aka yi na majalisar zartawa na jam’iyyar an zabi Ajibola Bashiru matsayin sakataren jam’iyar na ƙasa.
Manyan yan jam’iyyar APC ciki har da mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima na wurin da aka tabbatar da Ganduje matsayin sabon shugaba.
Dakta Ganduje ya kasance tsohon gwamnan Kano daa ya jagoranta shekaru takwas, sannan ya yi mataimakin gwamna shekara takwas haka kuma ya jagoranci hukumomi da tsarin gudanarwar mulki a wurare da dama.