Helilwatar tsaro a Najeriya ta ce babu wani zaɓi da ya rage musu illa amfani sa ƙarfin mulkin soji don kwatar mulki daga hannun sojin Nijar.

Daraktan yaɗa labarai na hukumar Tukur Gusau shi ya bayyana haka a helikwatar tsaro da ke Abuja ranar Alhamis.

Ko da dai ya ce har yanzu babu umarni daga shugabanni don fara ɗaukar mataki.

Ya ce za a ɗauki matakin da ya dace bayan kammala zaman tattaunawa na yini biyu wanda a halin yanzu ke gudana a Abuja.

Ya ce matakin da su ke nufi a ɗauka zai yuwu ne kadai bayan amincewar ƙungiyar ECOWAS da shugabaninta.

Ya kara da cewa matakin matakin da ya rage ƙungiyar ta ɗauka bai wuce na amfani da karfin soja ba don kwace mulki daga hannun soji a ƙasar Nijar.

Daraktan rundunar tsaron Najeriya ya ce aa halin da ake ciki sojin Najeriya ba su da wani iko na aiwatar da wani abu har sai sun samu umarni daga kungiyar a hukumance.

Ƙungiyar ECOWAS ta fara nuna yatsa ga sojin Nijar tare da barazanar amfani da karfin soji don tumbuke mulkin sojin kasar.

Sojojin sun hambarar da shugaba Muhammad Bazoum daga karagar mulki tare da nada sabbin shugabannin soji a matsayin gwamnoni bayan sun rushe shugabancin farar hula tare da kama wasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: