Sojin da ke mulki a jamhuriyar Nijar sun yi barazanaar hallaka hambararren shugaban kasar Mohammed Bazoum muddin sojojin makofta su ka yi yunkurin kwace mulki daga hannunsu.

Sojin sun yi baranar ne bayan da ƙungiyar ECOWAS ke ci gaba da shirin amfani da sojinta don kwace mulki daga hannun sojin.
Sojin Nijar sun gargadi kasar Amurka don ganin sun tsame hannunsu daga harkokin mulkin ƙasar.

Rahotanni sun bayyana yadda wasu kasashe kamar Mali da Burkina Faso na cikin shirin ko ta kwana bayan nuna goyon bayansu ga mulkin soji a Nijar.

Ƙungiyar ECOWAS ta sha alwashin amfani da soji wajen kwace mulki daga hannun sojin kasar Nijar.