Wasu gammayyar mabiya mazahabar shia a Najeriya reshen jihar kano sun fito a yau juma a don gudanar da zanga-zanga a fadin jihar.

Yan mazahabar shia an sun yi zanga zangar ne a manyan tituna dake fadin jihar ta Kano.
Sun dauke da kwalaye da tutaci ciki harda ta kasa Najeriya.

Suna tafiya a kasa wasu abun hawa suna bayyana cewa ba sa goyon bayan shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yaki yan uwansu yan Nijar don kuwa yan uwansu.

bayan da suke gudanar da zanga-zangar mujallar matashiya ta ziyarce su inda suka bayyana cewa umarni ne daga sama shiyasa suke muzaharar.
Babban darakatan mazahabar na jihar Kano malam Yakubu yayi mana karin haske wanda ya ce sun yi ne domin nuna damuwa tare da jan hankalin gwamnati don ganin tajanye ƙudirin.
Zanaga-zangar dai na zuwa ne bayan da shugaban kasashen ECOWAS suka bayar da umarni ta Hannin shugabanta bola Ahmed Tinubu cewa sojoji su shirya don yaƙar jamhuriyar Nijar.