Ƙungiyar kare haƙkin ɗan’adam ta Human Rigths Netowork ta ja hankalin gwamnatin tarayya a kan ɗaliban da za ta tura ƙasashen waje don yin karatun digiri na biyu.

Ƙungiyar ta ce maimakon tura ɗaliban ya fi dacewa gwamnatin ta mayar da hankali wajen biyawa ɗaliban da ke son yin karatun digirin farko a jihar.

A wata sanrwa da ƙungiyar ta aikewa Matashiya TV mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Kwamared AA Ayagi ya ce kuɗin da za a kashwa ɗalibi guda a ƙasar waje za a iya biyawa ɗalibai 30 su yi karatu a jami’o’i na Najeriya.

Sannan ya fi dacewa a mayar da hankali a kan waɗanda ba su yi karatun digiri na farko ba maimakon waɗanda sun yi na farko su ke son yin na biyu.

Haka kuma rashin mayar da hankali wajen tallafawa ɗaliban da su yi karatu a jihar na iya kai wa ga yawan masu aikata laifuka duba ga ƙarin kuɗin makaranta da aka samu a ƙasar.

Ƙungiyar ta shawarci gwamnatin Kano da ta yi duba wajen tura ɗaliban da za ta yi tare da mayar da hhankali zuwa ga abinda zai amfani ɗalibai da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: