Wasu da ake zargi masu garkuwa ne sun yi garkuwa da wasu mutane bakwai tare da hallaka mutum daya a cikin karamar hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin mai suna Isyaku Bungudu ne ya shaidawa Channels TV faruwar lamarin.

Bungudu ya ce masu garkuwar sun shiga yankin ne da safiyar yau Litinin dauke da muggan makamai.

Isyaku ya kara da cewa zuwan ‘yan ta’addan ke da wuya suka fara harbin sama domin tsoratar da mutanen yankin kafin daga bisani kuma suka hallaka mutum daya a yayin harbin.

Kazalika ya ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane bakwai ciki harda dan sarkin Bungudu Abdulrahman Hassan da wani ma’aikacin hukumar kula da harkar noma ta kasa da kasa IFAD Abubakar S/Fada.

Ishaq Bungudu ya koka kan yadda hare-hare ke kara kamari a hedkwatar karamar hukumar duk da kusancin garin Gusau babban birnin Jihar.

Bagudu ya kuma bukaci da gwamnan Jihar Dauda Lawal Dare da ya nada masu ba shi shawara a kan harkokin tsaro domin kawo karshen matsalar tsaro a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: