Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta kama wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi wanda ya bayyana cewa shi jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na Kasa NDLEA.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar Benjamin Hundeyin shine ya tabbatar da kama wanda ake zargin a ranar Lahadi.

Kakakin ya ce an kama mutumin ne dauke da kwayar Marsh-Mallow mai nauyin kilogiram hudu.

Benjamin ya bayyana cewa bayan kama wanda ake zargin rundunar ba ta tuntuɓi hukumar ta NDLEA ba domin tabbatar da cewa ko wanda ake zargin jami’inta ne.

Wata majiya daga jami’an an sandan ta bayyana cewa a binciken farko da aka gudanar wanda ake zargin ya bayyana sunansa a matsayin Kelechi Chukwumeeije, sannan yana aiki ne a ofishin NDLEA da ke a ƙofar farko ta tsibirin Tin-Can da ke jihar Legas.

Majiyar ta kara da cewa wanda ake zargin ya bayyana cewa wani na sama da shi ne ya ba shi ƙwayoyin da aka kamashi shi da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: