Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta kama wani dan fashi da makami mai suna Akeem Owonikoko wanda ya bayyana cewa wani Insfectan ‘yan sanda mai suna Ola ne yake kai musu bindigun da suke amfani da su gurin aikata ta’addanci.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Omolola Odutola ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi.

Kakakin ta ce an kama matashin ne akan babbar hanyar Sagamu zuwa Ijebu Ode a lokacin da jami’ansu tare da jagoroncin kwamandan yankin Ijebu Ode su ka kai sumame yankin.

Omolola ta kara da cewa an kama wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare a cikin wata mota kirar Toyota Camry a lokacin da ya nufi yankin Ijebu-Ode.

Inda suka bayan yunkurin kamasu da jami’an su ka yi suka tsere zuwa cikin daje su ka bar motar.

Kakakin ta kara da cewa bayan sun tsere jami’an suka gudanar da bincike a yankin, inda su ka yi nasarar kama Akeem wanda ya saka kayan jami’an tsaron sa-kai.

Ta ce bayan kama Owonikoko jami’an sun bincike motarsa inda suka samo kayayyaki na laifi da dama ciki harda wata bindiga ƙirar gida da kuma harsasai mabanbanta sama da guda 100.

Sannan Jami’ar ta ce jami’an ‘yan sanda sun je gidan dan fashin, inda suka gudanar da bincike harta kai ga sun gano karin wasu manyan makamai motoci da kuma miyagun kwayoyi.

Ta ce bayan sun kammala bincike za a aike da shi kotu domin yi masa hukunci.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: