Gwamna Jihar Zamfara Dauda Lawal Dare yayi wata ganawa da hafsan sojin Kasa Janar Taoreed Lagbaja a domin magance matsalar rashin tsaro da ta addabi Jihar.

Mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Idris ya ce ganawar na zuwa ne bayan da babban hafsan sojin ya je rangadin aiki a shiyyar Arewa maso Yamma.

Kakakin ya ce gwamnan ya gana da shugaban sojin ne a gidan gwamnati Jihar da ke garin Gusau, inda suka tattauna da gwamnan kan yadda za a karfafa hadin gwiwa tare da samar da hanyoyin yaki da matsalar ‘yan bindiga a jihar.

Sannan gwamnan da Janar Lagbaji sun samar da hanyar da za su inganta ayyukan soji domin dawo da cikakken zaman lafiya a fadin Jihar ta Zamfara.
A yayin jawabin Janar Lagbaja ya tabbatar wa gwamnan Jihar cewa nan da makonni masu zuwa jami’an soji za su gudanar da wani atisayen domin a Jihar domin yaki da ‘yan ta’adda.
