Wasu ‘yan bindiga sun hallaka wani ango da amaryarsa wadanda dukkaninsu malaman wata makarantar sakandire ne tare da jikkata mataimakin shugaban makarantar a garin Kwi cikin karamar hukumar Riyom ta Jihar Filato.

Sakataren yada labaran kungiyar Berom Youth Movemen ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sakataren ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Litinin.

Rwang ya kara da cewa mata da mijin da aka hallaka ba su dade da yin aure ba.

Sakataren ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne a lokacin da malaman makarantar su ka gudanar da taron akan yadda za su shirya taron bayar da kyautuka ga daliban makarantar a ranar Juma’a mai zuwa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar DSP Alfred Alabo ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema a ranar Litinin.

Kakakin ya ce sun fara gudanar da bincike domin gano wadanda su ka aikata hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: