Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta ayyana tafiya yajin aikin sai babatagani matukar farashin man fetur ya sake karuwa a Kasar.

Shugaban kungiyar na kasa Joe Ajaero ya tabbatar da hakan.
Joe Ajaero ya ce kungiyar kwadago ba za ta lamunci sabon karin farashi man fetur din da ake yunkurin yi ba.

Shugaban ya ce kungiyar NLC da TUC ta ‘yan kasuwa babu abinda zai hana su tafiya yajin aiki matukar kudin fetur ya sake tashi a Kasar.

Ajaero ya kara da cewa karin farashin man ka iya kara jefa ‘yan kasar cikin wahala baya ga wadda su ke ciki.
Kungiyar kwadago ta bayyana hakan ne bayan rahotannin da ke yawo cewa litar fetur za ta iya haura Naira 720 a kasar.
