Gwamnan jihar Neja Umar Bago ya ce da yawan manoma a jihar sun haƙura da yin noma sanadin fargabar kai musu hari daga ƴan bindiga.

Gwamna Bago ya bayyana haka ne yayin da shugaban hukumar kare fararen hula ta NSCDC na ƙasa Ahmed Audi ya kai masa ziyara a ranar Laraba.
Ya ce manoma da yawa sun ƙauracewa zuwa gonaki saboda fargabar kai musu hari daga ƴan bindiga.

Sai dai shugaban hukumar kare fararen hula ta NSCDC na ƙasa ya ce ya kai masa ziyara ne domin haɗa kai da sauran jami’an tsaro ta yadda za a magance matsalar tsaro da ta addabi jihar.

Ya ƙara da cewa jihar na buƙatar ɗaukin gaggawa daga jami’an tsaro a dalilin haka ne ma ya sa su ka kai ziyarar domin samar da wasu hanyoyin yadda za a kawo ƙarshen matsalar.
Sannan ya buƙaci gwamnan da ya samar da ƙarin ofisoshin hukumar a ƙananan hukumomi 26 na jihar ta yadda hakan zai ƙarfafi jami’an a kan aikinsu.
Gwamnan jihar Umar Bago ya ce jihar na da albarkar faɗin ƙasa wanda hakan zai zama mafita ga manoma wajen samar da abinci, amma hakan na haɗuwa ta cikar ganin yadda ake ƙara ɓullo da salon na ta’addanci a jihar.
Sannan ya yabawa shugaban hukumar a bisa ziyarar da su ka kai masa, tare da bayar da haɗin kai don kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar.
