Ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya IPMAN ta buƙashi shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi koyi da shugaban ƙasar Kenya wajen mayar da tallafin man fetur ko da na wucin gadi ne.

Ƙungiyar ta buƙaci shugaban da ya sassauta dokar cire tallafin la’akaci da farashin dalar amuruka da ke ciga da hauwa a ƙasar.
Sakataren ƙungiyar dilallan man ta ƙasa Mohammd Shu’aibu ya ce sun kula da yadda shugaban ƙasar Kenya ya mayar da tallafin man ganin halin da ƴan ƙasar su ka shiga bayan watanni biyu da cire tallafin a ƙasar.

Ya ƙara da cewa lokacin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana cire tallafin man fetur sun ankarar da gwamnatin a kan matsalar da hakan za ta haifar.

Ya ce a halin da ake ciki a yanzu, dilallan man fetur ba su da sha’awar cigaba da shigo da man daga waje, amma sassauta cire tallafin zai taimaka musu wajen cigaba da shigo da man cikin ƙasar.
La’akari da bayanan da kanfanin mai na Najeriya NNPC ya fiar a ranar Talata, na rashin niyyar ƙara farashin mai, ƙungiyar ta ce muddin farashin dala ya ci gaba da hauhawa, babu makawa za su goyi bayan ƙungiyar ƙwadago wajen tafiya yajin aiki da zanga-zanga a ƙasar.
Mohammed Shu’aibu ya ce farashin sufuri na ninka sau uku a ƙasar, kuma wannan lokaci ne ya fi dacewa gwamnati ta shiga lamarin ganin yadda komai ke cigaba da hauhawa.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire tallafin man fetur ne tun a lokacin jawbainsa bayan shan rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayun shekarar da mu ke ciki.
