A wani labarin kuma rundunar sojin saman Najeiya ta musanta bidiyon da ake yaɗawa cewar ƴan bindiga ne su ka harbo jirgin jami’ansu da ke aikin ceto a jihar Neja.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magan da yawun rundunar Air Coomodore Edward Gabkwet ya sanyawa hannu a yau Laraba.
Ya ce ce farfagabda ce da ƴan bindigan ke yaɗawa domin kawo ruɗani a cikin jama’a.

Kakakin ya buƙaci a yi watsi nda bidiyon da hotunan da ake yaɗawa ganin yadda jami’ai da iyalan mamatan za su ji.

Rundunar ta ce hankalinta ya kai kan faifen bidiyo da ake yaɗawa a kafofin sa da zumunta kan wani bidiyo da wasu ke iƙirarin harboshi daga sama.
Sanarwar ta nuna takaici a kan hatsarin jirgin saman wanda ta ce ta rasa wasu daga cikin jami’anta a sanadin hatsarin jirgin.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da bincike domin gano haƙiƙanin dalilin faɗuwar jirgin.
A ranar Litinin ne hukumar sojin samar Najeriya ta ce jirginta ƙirar helikwafta mai lamba MI-171 ya yi hatsari a ƙauyen Chikuba da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.
