Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa jami’an sojoji 36 ne aka hallaka a Jihar Neja.

Daraktan yada labarai na rundunar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Buba ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke bayyana adadin mutanen da aka kashe a harin kwanton ɓaunar da aka kaiwa jami’an sojin a Jihar ta Neja a ranar Litinin.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa rundunar ta bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da aka saba yi sau biyu a mako.

A yayin wata tambaya da aka yiwa Buba ya bayyana cewa suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano musababbin hadarin jirgin.

Buba ya kara da cewa babu kungiyar da za ta iya kaiwa dakarun sojojinta hari kuma su ci bulus.

Leave a Reply

%d bloggers like this: