Ƙungiyar Tarayyar ƙasashen Afrika AU ta cire jamhuriyar Nijar daga cikinta sakamakon juyin mulkin da sojoji su ka yi a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

Ƙungiyar ta dakatar da dukkan ayyukan cigaba da ya shafi ƙasar Nijar har sai komai ya daidaita a kan rikicin da ke faruwa.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a yau Talata, ƙungiyar ta ce ta cire ƙasar Nijar daga cikinta ne bayan da sojoji su ka ƙi amincewa da mayar da shugaba Bazoum muƙaminsa.

An dakatar da ƙungiyar bisa saɓawa ƙa’idar ƙungiyar na wanzar da zaman lafiya, tsaro, haɗin kai, da kuma demokaraɗiyya.

Sannan ƙungiyar ta buƙaci sairan ƙungiyoyin duniya da dukkannin ƙasashen da su ka haɗa kai wajen samar da cigaban ƙasar da su yanke dukkan hulɗa da Nijar wanda ta ayyana mulkin sojin a matsayin ramatacce.

Ƙungiyar ta AU ta jinjinawa ƙungiyar cigaban tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ECOWAS bisa ƙoƙarin da ta ke na dawo da mulkin demokaraɗiyya a ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: