Sabon ministan tsaro a Najeriya Alhaji Badaru Abubakar ya sha alwashin magance matsalar tsaro cikin shekara guda.

Muhammad Badaru ya ce nan da shekara ɗaya matsalar tsaron da ake fuskanta a ƙasar za ta zama tarihi.

Badaru ya bayyana haka ne a helkwatar tsaro ta ƙasa wanda ya alƙawarta kawo sauyi mai yawa a ɓangaren.

Ya ce zai samar da tsarin ganawa da manyan hafsoshin tsaron Najeriya kowanne wata, domin samar da sabbin dabarun yaƙi da matsalar tsaro a Najeriya.

Haka kuma sabon ministan ya buƙaci samun dukkan bayanai daga jami’an tsaro, domin samar da mafita a kan matsalolin da ake fuskanta a ƙasa.

A yayin da yake nasa jawabin, babban hafsan tsaron ƙasa Janar Chirtoper Musa ya sha alwashin dawo da zaman llafiya a ƙasar.

Ya ce a matsayinsa na ɗan Najeriya wajibi ne su dage don ganin an dawo da mataba da zaman lafiyan da aka rasa a ƙasar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabbin ministocin da ya naɗa su 45 a Abuja ranar Litinin domin taimaka masa wajen tafiyar gwamnatinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: