Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake aikewa da tawagar malaman zuwa jamhuriyar Nijar domin sake ganawa da shugabannin mulkin sojin ƙasar.

Matakin hakan na zuwa ne bayan da shugaban ya gana da malaman a fadarsa da ke Abuja yau bisa jagorancin Sheik Ɗahiru Usman Bauchi.
Shugaba Tinubu ya sake aike da tawagar malaman ne domin shiga tsakani ganin an samar da sasanci wajen dawo da mulkin demokaraɗiyya maimakon amfani da ƙarfin soji.

Karo da biyu ke nan da tawagar malaman za ta gana da shugannin mulkin sojin Nijar yadda za a samar da sasanci.

A zaman da shugaba Tinubu ya yi da malaman a yau sun ba shi bayani a kan ganawar da su ka yi da shugaban mulkin sojin a ziyararsu ta farko.
Ko a ranar Talata sai da shugaba Tinubu ya gana da tawagar shiga tsakani da ƙungiyar ECOWAS ta tura ƙarƙashin tsohon shugaban Najeriya Janar Abdussalam mai ritaya.
Sojoji a jamhuriyar Nijar na ci gaba da shan matsin lamba daga ƙungiyar ECOWAS da sauran manyan ƙasashen duniya tun bayan da su ka karɓe ikon mulkin ƙasar a ranar 26 ga watan Yuli da ya gabata.