Ma’aikatar harkokin ƙasashen waje a jamhuriyar Nijar sun musanta batun korar jakadun ƙasashen Najeriya Amuruka da wasu kasasheo;u\\ daga ƙasar.

Wasu takardu ɗauke da sa hannun tambarin ma’aikatar harkokin ƙasashen wajen Nijar ne su ka fara yawo a jiya Juma’a a kafofin sa da zumunta wanda su ka bai wa jakadun kwanaki biyu don ficewa daga ƙasar.
Sai dai shugabannin mulkin sojin ƙasar sun musanta batun korar jakadun daga ƙasar a yau Asabar.

Ma’aikatar harkokin ƙasashen wajen ta ce jakadan ƙasar Faransa kaɗai ta baiwa umarnin ficewa daga ƙasar.

Ganin yadda takardun ke yawo a jiya ake zargin danganta ta kuma yin tsami tsakanin Najeriya da Nijar bisa zargin matakin amfani da soji da ƙungiyar ECOWAS ke shirin yi wajen karɓe ikon mulkin ƙasar daga hannun soji.
Idan ba a manta ba hukumomin ƙasar Nijar sun yarje ƙasashen Burkina Faso da Mali su aike da sojojinsu ƙasar domin taimaka musu daga harin dakarun ECOWAS.