Aƙalla mutane da dama ne su ka rasa rayuwarsu yayin da aka kai hari garin Chito a ƙaramar hukumar Ukum a jihar Benue.

Rahotanni sun ce an gano gawar mutane biyar daga cikin waɗanda su ka rasa ransu a wani hari da aka kai a baya bayan nan.

Ƴan bindigan na hallaka mutanen da su ka ƙi biyan haraji a wata kasuwa da ke garin.

Wani shaida a garin ya ce kisan gillar da aka yi a ranar Juma’a ramuwar gayya ce da wasu ƴan bindiga su ka kaiwa wata tawagar daban.

Wani lauya da ya taso a garin ya yi kira da a saka dokar ta ɓaci domin samun damar daƙile ayyukan ƴan bindiga a garin.

A wata wasiƙa da ya aikewa manema labarai ya ce a ranar 25 ga watan Agustan da mu ke ciki sai da yan bindigan su ka hallaka mutane Takwas a garin na Chito da ke ƙaramar hukumar Ukum a jihar.

Sai dai sun zargi ƴan ƙabilar Tiv da yin mummunan aikin.
Daga jami’an ƴan sanda a jihar sun ce ba su samu labarin harin da aka kai garin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: