Jagoran yan awaren Najeriya Nnamdi Kanu ya ce ba zai roki gwamnatin tarayya ta sa baki don sakinsa ba.

Nnamdi Kanu ya bayyanna haka ne cikin wata wasika da magoya bayansa su ka rubuta a ranar 25 ga watan Agustan da mu ke ciki.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Mike Ozekhome wanda babban lauya ne, an fitar da ita a yau Talata 28 ga watan Agusta.

Lauyan ya nuna damuwa a kan yadda hukumar tsaro da DSS ke cigaba daa tsare Kanu.

An kama Nnamdi Kanu ne dai bisa zargin cin amanar ƙasa ta’addanci da kuma mallakar makamai.
Sai dai a baya kotu ta bayar daa umarni domin ya gana da likitocinsa.
Jagoran ƴan awaren IPOB na ƙoƙarin ballewa daga Najeriya tare da kafa ƙasar BIAFRA.
Kuma ake zargin ƙungiyar IPOB da ayyukan ta’addanci a Najeriya.