Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana juyin mulkin ƙasar Gabon a matsayin annoba da ta kama nahiyar Afrika.

Tinubu wanda ya magantu dangane da juyin mulkin da ya faru a safiyar yau Laraba, ya ce shi da sauran shugabanni za su mayar da martani dangane da juyin mulkin.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu a yau, ya ayyana juyin mulki da cewar wata annoba ce ta kama nahiyar Afrika.

Tinubu ya nuna damuwa a dangane da juyin mulkin da sojin su ka yi a yau.

An hamɓarar da shugaba Ali Bongo tare da tsareshi yayin da aka kama ɗansa kuma makusanci a gareshi.
Hakan na zuwa ne yayin da ƙungiyar ECOWAS ke ƙoƙarin lalubo hanyar warware matsalar juyin mulki a jamhuriyar Nijar.
Juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.