Gwamnatin tarayyar Najeriya ta shawarci wasu gwamnonin ƙasar da su kwashe mutanensu daga wani yanki don gudun rasa rayuwarsu.

Ministar jin ƙai da rage raɗaɗin talauci a Najeriya Betta Edu ce ta buƙaci a kwashe wasu mutane da ke kusa da teku Benue don tseretar da rayuwarsu.

Hakan ya biyo bayan zargin samun ambaliyar ruwa bayan ɓallewar tekun da ake zargi na iya shafar mutanen da ke maƙoftaka da wajen.

Ministar ta gargaɗi gwamnonin da su mayar da hankali domin buɗe dam ɗin Lagdo da ke ƙasar Cameroon na iya haifar da ambaliyar ruwan mai tsanani.

Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya NEMA ta bayyana a ranar Lahadi cewar, ambaliyar kai tsaye na iya shafar jihohin Benue, Kogi, Nassarawa Adamawa da jihar Taraba.

Sai wasu jihohi da lamarin na iya shafa kamar Bauchi, Cross River, Gombe, Delta da jihar Plateau.

Hukumar ma ta yi kira ga gwamnonin jihohin da su kwashe al’ummarsu daga yankunan da abin ka iya shafa domin tseratar da rayuwasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: