Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ƙaddamar da runduna ta musamman domin yaƙi da masu garkuwa da mutane tare da kawar da ayyukan ta’addanci a ƙasar.

Hafsan sojin kasan Najeriya Lafanal Kanal Taoreed Lagbaja ne ya bayyana haka ranar Talata.

Ya ce rundunar za ta ci gaba da matsawa har sai ta ga an kawar da dukkan ayyukan ta’addanci a ƙasar.

Ya ce za su tabbata dukkanin jami’an sun ruɓanya koƙarinsu a kowacce shiyya.

Ko a yankin kudu maso kudu ya ce za a tabbatar doka da oda sun koma aiki don jama’a su samu zaman lafiya.

Rundunar za ta yi amfani da kwarewa da kuma makamai na musamman ta yadda za a ci gaba da lissafa ƙoƙarinta.

Babbaan hafsan sojin ya ce hankalin hukumar ya koma kan garkuwa da mutane, ta’addanci, Faɗan manoma da makiyaya, da sauran muggan ayyuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: