Wani rahoto ya nuna cewar mutane 936 ne su ka rasa rayuwarsu sakamakon kifewar jirgin ruwa a Najeriya.

Rahoton wanda aka tattara na shekara uku da rabi, ya nuna yadda hatsarin jirgin ruwa ya salwantar da rayuka da dama.
Wannan na zuwa ne bayan da aka sake samun kifewar wani jirgin ruwa a jihar Adamawa wanda aka gano gawaarwakin mutane 11 yayin da ake ci gaba da aikin ceton wasu.

Ko a ranar Lahadi sai da aka yi asarar rayuwar mutane sama da 30 a jihar Neja duka a sanadin kifewar jirgin ruwa.

Jihohin da binciken ya nuna na mutuwar mutane sama da 900 a Najeriya akwai Adamawa, Kebbi, Kwara, Nejaa, Legas, Nassarawa, Akwa Ibom.
Sauran su ne Anambra, Cross River, Bauchi, Sokoto, Benue, Bayelsa, Kano, Ondo, da jihar Taraba.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggawa domin yin bincike a kan sanadin haɗɗuran jirgin ruwa da ake fuskanta a ƙasar.
Mutane 216 ne dai su ka rasa rayuwarsu sanadin kifewar jirgin ruwa a shekarar 2023 da mu ke ciki.