Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya NEMA ta gargadi wasu jihohi a Najeriya da ka iya fuskantar ambaliyar ruwan sama.

Hukumar ta ce jihohin 13 da wasu yankuna 50 mafi yawa a arewacin ƙasar na iya fuskantar ambaliyar ruwa a nan kusa.
A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce ambaliyar na iya farawa daga ranar 13 zuwa ranar 17 ga watan da mu ke ciki.

Mista Ibrahim Farinloye da ke zama wakilin sanya idanu na hukumar a jihar Legas shi ya bayyana haka yau Laraba.

Ƙananan hukumomin da za su fuskanci ambaliyar akwai Ƙaramar hukumar Sulaima da Ƙunci a jihar Kano.
Sai Bindawa da Jibia a jihar Katsina, da kuma Argungu a jihar Kebbi.
Sauran su ne. Neja da Kwara, Zamfaraa Taraba da jihar Bauchi.
Haka kuma akwai Adamawa da Yobe, sai jihohin Jigawa, Gombe da Borno.
Hukumar ta gargaɗi mutanen yankunan da su kula, tare da ɗaukar matakan da ka iya rage asara sanadin ambaliyar a nna gaba.