An samu daukewar wutar lantarki a fadin kasa Najeriya.

Kamar yadda wata sanarwar ta fito daga hukumar Samar da wutar lantarki TCN a jiya Laraba da misalin karfe 12:40 na dare.

Hakan na zuwa ne bayan da babban kamfanin samar da wutar ta lantarki TCN ya cika shekara ba tare da an samu daukewar wutar lantarki ba a kasar.

Sannan an bayyana cewa wutar lantarki ta dawo izuwa megawat 273 shiyasa aka samu matsalar wutar a kasar baki daya.

Sai dai har yanzu ana so a ji ta bakin shugaban hukumar ta TCN domin magantuwa akan lamarin wutar lantarkin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: