Mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara na musamman akan matasa da wasanni Yusuf Imam Ogan Boye ya bayyana cewa a shirye suke su mutu akan koma waye da ya yi yunƙurin taɓa kujerer gwamnatin Kano.

Ogan Boye ya bayyana haka ne a jiya Alhamis lokacin da yayi Hira da yan jaridu.
Ya ce sun shirya mutuwa su magoya bayan kwankwasiyya akan tafiyasu kuma a shiye suke da wannan tsarin.

Ya ce kuma babu wanda ya Isa ya kwace musu mulkin jiha don sune suka lashe zaben gwamnan jihar kano.

Ya ƙara da cewa babu gudu babu ja da baya game da tafiyar ta kwankwasiyya don kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu cikin kwana 100 da Abba Gida-Gida yayi a mulkin.
Daga Karshe Ogan Boye yace yana mai jan hankalin yan tafiyasu ta kwankwasiyya da su bude idanu su a tafiyar babu wanda zai iya fashin kujerar gwamnatin Kanon ko da su na da sama.