Hukumar jami’ar gwamnatin tarayya da ke jihar Legas sun sanar da rage kudin makaranta, bayan sun yi zama da babbar kungiyar dalibai ta kasa a jiya Alhamis.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, hukumar makarantar ta yi zama da zababbun shugabannin kungiyar daliban ta kasa a yammacin jiya Alhamis.

Jawabin da aka bata ya bayyana cewa “Hukumomin jami’ar Legas karkashin jagorancin shugaban jami’ar Farfesa Folasade Ogunsola, a ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba shekarar 2023, sun yi zama da shugaban kungiyar dalibai ta kasa Kwamared Usman Umar Barambu bisa rakiyar manyan jagororin kungiyar, da kuma shugabannin tsangayu na jami’ar Legas da suka fito daga tsangayoyi guda 9 da kwalegin Kiwon Lafiya.”

Jawabin ya kuma nuna cewa yayin gudanar da zaman, Barambu ya nuna yadda dalibai suka da nuna bukatar da ta hadar da janye kudin da aka kara, kudin dakunan kwana, da kuma dawo da kungiyar gudanarwar dalibai ta makarantar.

Sannan shugaban jami’ar Farfesa Ogusola, ya bayyana burin jami’ar shi ne samar da nagartaccen ilimi ga dalibai, ba tare da la’akari da banbancin yare ko kabila ba.

Bayan an yi duba na tsanaki ga bukatun dalibai an cimma matsaya kamar haka yayin zaman, kudaden da ake cajin dalibai na bukatuwar yau da kullum an rage shi daga Naira dubu 20 zuwa Naira dubu 15.

Kudin rajistar karatu ga kowanne dalibi ya ragu daga Naira dubu 126,325 zuwa Naira dubu 116,325 ga kwasa-kwasan karatun da basa bukatar dakin gwaje-gwaje ko na’urori. Sai kuma ragin kudi daga Naira dubu 176,325 zuwa Naira dubu 166,325 ga kwasa-kwasan da suke bukatar dakin yin gwaje-gwaje da na’urori.

Kudin rajistar daliban da zasu tafi aji na gaba kuwa ya ragu daga Naira dubu 100,750 zuwa Naira dubu 80,750 ga kwasa-kwasan da basa bukatar dakin yin gwaje-gwaje da na’urori.

Sai kuma kudin rajistar daliban da zasu tafi aji na gaba ga kwasa-kwasan da suke bukatar dakin yin gwaje-gwaje da na’urori, ya ragu daga Naira dubu 140,250 zuwa Naira dubu 120,250.

Sai kuma kwasa-kwasan kimiyyar lafiya, hada magunguna da harkokin lafiya, ya ragu daga Naira dubu 190,250 zuwa Naira dubu 170,250.

Kudin bikin yaye dalibai kuma ya ragu daga Naira dubu 30 zuwa Naira dubu 27, sai dakunan kwanan dalibai inda aka rage su daki-daki, ragin Naira dubu 47, Naira dubu 55, da kuma Naira dubu 115.

A watan Yulin da ya gabata ne dai jami’ar Legas din ta sanar da karin kudin makarantar ga sabbin dalibai da masu tafiya zuwa aji na gaba, bisa dalilin da suka alakanta da matsin tattalin arziki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: