Rahotanni daga baban birnin tarayyar Najeriya Abuja na tabbatar da cewar kotun ƙoli ta kama da wuta.

Ofishin alƙalai uku aka ruwaito sun ƙone bayan tashin gobarar.
Godan jaridar Arise ya ruwaito cewar, wutar ta kama wai ɓangare na cikin kotun.

Sai dai ba a san sanadin tashin gobarar ba.

Wannan dai itace gobara da aka yi a kusa-kusa wadda ta shafi ofishin gwamnati.
Ko a watan Mayun shekarar da mu ke ciki, gobara ta kama a rundunar sojin samar Najeriya.
Yayin da a shekarar da ta gabata ta 2023 ma’aikatar kuɗi ta tarayya wani ɓangare ya kama da wuta.
