Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ta ce kashi 50% na ɗaliban da ke karatu na iya ajiyewa saboda tsadar karatu da ake ciki a ƙasar.

Shugaban ƙungiyar Frafesa Emmanuel Osodoke ne ya bayyana haka ya ce nan da shekaru biyu zuwa uku masu zuwa ɗaliban da ke karatu a jami’o’in ƙasar kashi 50% daga ciki na iya ajiye karatun nasu.
A wata hira da aka yi da shugaban a gidan talabiji na Channels ranar Lahadi da daddare, ya gargaɗi ɓangaren ilimi na ƙasar da su farga a kan abinda ka iya faruwa.

Sai dai ya alaƙanta ƙara kuɗin da jami’o’i su ka yi da mafi ƙarancin albashin da ake biya na naira 30,000 a ƙasar.

Sannan ya ce akwai hatsari mai yawan gaske idan aka samu ƙarin matasa masu yawa da su ka bar makaranta.
Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata gwamnatin Najeriya ta ce ta ƙarawa malaman jami’a albashi da kashi 30 ga masu matsayin farfesa.
