Gwamnatin Najeriya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu ga ma’aikata na ƙasar.

Haka na ƙunshe a wata sanawar da ma’aikatar harkokin cikin gida babban sakataren ma’aikatar ya fitar ranar Litinin a madadin ministan.
Sanarwar ta ce an bayar da hutun ne domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam.

Gwamnatin ta buƙaci musullmi da su yi koyi da halayen Annabin tsira annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam musamman tausayi, jin ƙai, soyayya da haƙuri.

Sannan ta buƙaci ƴan ƙasar da su yi amfani da hutun wajen sanya ƙasar cikin addu’a musamman a kan harkokin tsaro da sauran al’amura.
Kuma gwamnatin ta buƙaci al’ummarta da su ci gaba da bai wa shugaba Bola Tinubu haɗin kai domin tabbatar da ayyukan ci gaba a ƙasar.
