Gwamnatin jihar Zamfara ta zargi gwamnatin tarayya da tattaunawa da ƴan bindiga a jihar..
Gwamnatin jihar ta ce akwai wata tawaga da gwamnatin tarayyar ta tura kuma ake zargi sun fara tattaunawa da ƴan bindiga.
Sannan ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta gudanar da bincike a kan wasu hukumomi na wata tawaga da su ka fara tattaunawa da ƴan bindigan.
Gwamnan jihar Dauda Lawal Dare ne ya bayyana haka yau Litinin a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sulaiman Bala Idirs ya fitar.
Sanarwar ta alaƙanta hakan da zagon ƙasa a kan yunƙurin da gwamnatin jihar ke yi na magance matsalar.
Gwamnan ya ce yunƙurin yin sulhu da gwamnatin da ta shuɗe ta yi bai yi wani tasiri ba, a don haka ba za su lamunci sulhu da ƴan bindigan ba.
Daga cikin matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka akwai dakatar da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
Wannan mataki na zuwa ne bayan da aka sace wasu ɗaliban jami’ar Tarayya ta Gusau a jihar ranar Juma’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: