Rundunar yan sanda a jihar Abia sun sha alwashin kama mutanen da su ka hallaka wani mutum mai shekaru 65 a duniya.

 

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar ASP Maureen Chinaka ta bayyana haka a wata sanarwa da ta aikewa da manema labarai.

 

Ta ce an samu gawar mutumin mai suna Chigbu Chigoze a safiyar ranar 21 ga watan Satumban da mu ke ciki.

 

Sannan sun sameshi ncikin cjini bayan rauni da aka yi masa, kuma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.

 

Tuni jami’an su ka fara bincike a kan gawar mutumin bayan da aka aike da ƙorafin zuwa sashen binciken maiyan laifuka da kisan kai.

 

Sannan sun buƙaci da a gabatar musu da rahoton duk wani da ya san wani abu dangane da mutuwar mutumin don ganin an sanarwa da jami’an ƴan sanda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: