Gwamnatin Najeriya za ta raba naira 50,000 ga mutane miliyan 1.5 kowanne.

Gwamnatin ta fito da shirin ne domin baiwa ƙananan ƴan kasuwa mata don bunƙasa kasuwancinsu.


Tallafin da bashi ne za a bayar ne ba tare da sanya kuɗin ruwa domin biya ba.
Ministar jin kai a Najeriya Dakta Beta Edu ce ta bayyana hak ayayin da ta ziyarci ministan yaɗa labarai Muhammed Idris a ofishinsa ranar Talata.
Ministar ta ce tuni aka fara tantancewa tare da shigar da bayanan mutanen da ka iya amfana.
Kuma rukunin farko na tsarin zai shafi kasuwanni 109 ne na faɗin Najeriya.