Kungiyar Kwadago a Najeriya (NLC) ta bayyana yawan adadin mafi karancin albashi da za su tattauna da Gwamnatin Tarayya a nan gaba.

Kungiyar ta ce akalla gwamnatin sai ta biya Naira dubu 100 zuwa 200 a matsayin mafi karancin albashi ganin yadda komai ke tsada.


Kungiyoyin kwadago sun shirya shiga yajin aiki a jiya Talata 3 ga watan Oktoba bayan cire tallafin mai a kasar.
Daga bisani su ka janye bayan sun yi wata ganawa da Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin 2 ga watan Oktoba a Abuja.
Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero ya ce sun daga yajin aikin ne don bai wa gwamnatin lokaci don cika alkawuran da ta dauka.
Ya ce daga alkawuran akwai Naira dubu 35 da za ta kara wa ma’aikata a matsayin rage radadin cire tallafi inda ya ce mafi karancin albashin na iya kai wa Naira dubu 200.
Ya bayyana cewa wannan dubu 35 da aka kara an dora shi ne kan mafi karancin albashi na da na Naira dubu 30 inda ya ce za su duba abubuwa da dama yayin tattauna sabon mafi karancin albashi.