Wasu miyagu ɗauke da makamai da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne, sun kai farmaki a ɗakunan kwanan ɗalibai na jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a yayin harin, ƴan bindigan sun yi awon gaba da ɗalibai mata na jami’ar guda biyar.


Lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, a ɗakunan kwanan ɗalibai na wajen makaranta da ke bayan makarantar Mariamoh Ajiri, kusa da kasuwar Laraba a Dutsinma.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, babu wani bayani dangane da halin da ɗaliban ke ciki, domin waɗanda suka yi garkuwa da su ba su tuntubi iyalansu ba.
Ɗalibai sun tabbatar da cewa sakamakon wani abu makamancin haka da ya faru a jami’ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, hukumar ta FUDMA ta umurci dukkan daliban da su dai na fitowa waje daga ƙarfe 10 na dare.
Shugaban sashin hulda da jama’a na jami’ar Habibu Umar Aminu ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na daren ranar Laraba, inda ya ƙara da cewa ana cigaba da ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Sadiq Aliyu Abubakar, ya ce an kama mutum ɗaya da ake zargi da bayar da bayanai ga ƴan bindigan.