Majalisar dinkin duniya na cigaba da nuna damuwa kan rikicin Isra’ila da Hamas a Gaza wanda ake samun karuwar mutanen da ke rasa rayuwarsu.

 

Zuwa yanzu dai dubban mutane ne su ka rasa ransu a sakamakon rikicin bayan hare hare da aka kaiwa kowa.

 

Babban sakatare a majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya nuna takaici a kan rikicin wanda ya yi silar mutuwar mutane da yawa.

 

Sakataren ya yi Alla-wadai da rikicin wanda mayakan Hamas ke rike da israilawa sana da 200 a hannunsu.

 

Sai dai a ranar litinin an saki mutane biyu daga cikinsu.

 

Isra’ila na ci gaba da kai hare hare Gaza wanda Hamas ta ce an kashe mutane 5,800 daga rabar 7 ga watan Oktoban da mu ke ciki.

 

Yayin da aka kashe israilawa 1,400 wanda adadinsu ya kai sama da 7,000 zuwa yanzu.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: