Sojojin Amurka sun tabbatar da cewa sun kai hare-hare ta sama a wasu wurare biyu inda sojin Iran ke amfani da su a Syria.

Sakataren tsaron Amurka Lyod Austin, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce hare hare ne na kare kai.


Lyod ya kara da cewa hare haren da dakarun nasu su ka fara kai wa wani martani ga kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran wanda har hakan ta haifar da kai hari ga sojin Amurka a ranar 17 ga watan Oktoban da muke ciki.
Akalla sama da mako guda kenan dakarun sojin Amurka ke cigaba da kai zafafan hare hare kan kungiyoyin da suke samun goyon bayan kasar Iran.
Ko da ma’aikatar tsaron kasar ta Amurka Pentagon ta tabbatar da cewa an kai wa kawancen da Amurka ke jagoranta a Iraqi da Syria hari sama da sau 16 cikin wannan watan na Oktoba.