Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi Jigawa, ya roki gwamnatin tarayya ta gaggauta kammala aikin noman ranin kwari da ke jiharsa.

Gwamna Umar Namadi ya bukaci a karasa aiki domin a bunkasa noma a jihar Jigawa.

Gwamnan ya ce shekaru kusan 40 da su ka wuce aka fara aikin a lokacin mulkin Shehu Shagari, amma har yau ba a iya kammalawa ba.

Gwamnatin Marigayi Shugaba Shehu Shagari ta kawo tsarin noman ranin ne da nufin inganta noma domin a iya samun isasshen abinci.

Rahoton ya ce gwamnan ya yi wannan bayani wajen kaddamar da tsarin noman alkalama na kasa wanda za ayi a Hadejiya dake jihar Jigawa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: