Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA, ta yi holin miyagun kwayoyi na kimannin Naira Miliyan 210 da katan din taliyar yara guda 100, Da allura da sauran kayayyaki

Kakakin Hukumar Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa ne ya bayyana hakan, a wata ganawa dayayi da ‘yan jaridu a Shalkwatar Hukumar a yau Litinin.
Nabilisi ya ce, cikin abinda Hukumar ta kama harda Maganin karfin maza, da allurar dake gusar da hankali, dama nau’ikan kayan kwalam da makulashe na yara.

Shugaban hukumar ta KAROTA Injiniya Faisal Muhmud Kabir yayi kira ga al’umma wajen kula da abinda zasu saya na ci ko na sha, domin tabbatar da cewar basu sayi kayan da wa’adin amfaninsa ya kare ba, don gudun fadawa barazana ga lafiyar yara da ma al’umma baki daya.

Ya ce ko a makon da ya gabata, sun sami labarin wani daya sha kwaya kuma daga karshe tayi sanadiyyar rasa ransa.