Ministan shari’a a Najeriya, Lateef Fagbemi (SAN) ya bukaci ‘yan Najeriya da su goyi bayan ayyukan gyara kasa da Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ya keyi.

Ya kuma bayyana bukatar ‘yan Najeriya da su yi hakuri da shugaban kasa, inda yace ayyukan da ya dauko za su haifarwa Najeriya babban cigaba.
Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi ta bakin hadiminsa a fannin yada labarai, Kamarudeen Ogundele.

Da yake jawabi a wani taron ahalinsa a garinsu Ijagbo a karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara, ya ce dole ne a yi hakuri idon anaso aga daidai.

A cewarsa, ‘yan Najeriya da za su yi hakuri, shugaban kasa a shirye yake ya fitar da Najeriya daga duhun da take ciki.
A yunkurin sa na kawowa Najeriya ci gaba ana rantsanrdashi ya fara neman hanyar da kowani dan kasa zai samu jindadi da walwala.