Majalisar dokokin Najeriya ta dauki mataki na tabbatar da cewa ta samar da wadatattun kudade don yaki da cutar kanjamau a Najeriya.

Shugaban kwamitin yaki da kanjamau, tarin fuka da zazzabin cizon sauro na majalisar, Amobi Oga, ya sanar da hakan a Abuja, a shirin ranar cutar kanjamau ta duniya na shekarar 2023.
Ana gudanar da bikin ranar kanjamau ta duniya a ranar 1 ga watan Disamba na kowacce shekara, domin wayar da kai da kuma tuna wa da wadanda cutar ta kashe.

Oga, wanda wakili ne na mazabar Umuneochi a majalisar tarayyar, ya tabbatar da cewa za su tallafawa hukumar yaki da cutar kanjamau don dakile yaduwar ta.

Haka zalika ya yi alkawarin samar da wata doka a majalisar da za ta kare ‘yancin mutane masu dauke da cutar kanjamau don kare su daga tsangwamar jama’a.
Daraktan hukumar NACA, Gambo Aliyu ya ce akalla ‘yan Najeriya miliyan 1.8 ke rayuwa da kanjamau, yayin da miliyan 1.63 ke karbar maganin rigakafin cutar.
Da ya ke magana kan taken bikin ranar na wannan shekarar, Aliyu ya bayyana muhimmiyar rawar da al’umma za su taka wajen yaki da cutar kanjamau.