Shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote ya tabbatar da cewa matatarsa ​​mai ƙarfin tace litar ɗanyen man fetur 650,000 ta shirya tsaf domin fara tace man fetur na farko a cikin watan Disamba.

Hamshaƙin attajirin ya bayyana cewa, burin farko shine a samar da ganga 350,000 na man fetur a kullum daga matatar man.

Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da Financial Times a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, 2023.

Ya ce matatar wacce ta gaza fara aiki a lokacin da aka tsara har sau biyu, za ta fara ne da ganga 350,000 a kowace rana, inda ya ce tuni aka cimma matsaya kan fara jigilar ɗanyen mai kusan ganga miliyan shida a watan Disamban 2023.

A cewar sa Za su fara da ganga 350,000 a rana, bai sani ba ko wasu mutane za su iya tsira idan suka fuskanci irin ƙalubalen da suka fuskanta.

Dangote ya bayyanawa masu zuba jari a ƙasar Saudiyya a wata ziyarar da ya kai ƙasar tare da shugaban ƙasa Bola Tinubu cewa matatar ta na son ta fara aiki da ɗanyen mai daga kamfanin mai na NNPC.

An samu rahotannin cewa matatar ta yi odar ɗanyen man fetur ganga miliyan shida daga NNPC, jimillar ganga 200,000 a kullum.

Dangote ya shaidawa manema labarai cewa ya yi amanna cewa matatar za ta iya tace ganga 650,000 a kowace rana nan da ƙarshen shekarar 2024.

Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirika ya ce matatar ta samu nasarar magance duk wasu ƙalubalen da suka shafi samar da ɗanyen mai, inda ya ce a ƙarshe za a sanya ta kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Legas.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: