Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta tabbatar da kama wasu mata da ake zargi da hannu wajen yin zanga-zanga da aka haramta yi a jihar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Muhammad Usaini Gumel ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai yau Litinin, a shallkwatar rundunar da ke unguwar Bompai a Kano.
Ya ce rundunar ba ta kama mutanen da nufin ƴan wata jam’iyya ba, sai don karya doka ta haramta kowacce zanga-zanga a jihar.

Sannan sun nesanta kansu da jinginasu da wasu ke yi da siyasa, wanda ya ce sam hakan bashi da tushe balle makama.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da aikin tsare rayuwa, lafiya da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a jihar Kano.
Wakilinmu Ahmad Murtala Ibrahim ya bamu labarin cewa, taron ya samu halartar turawan ƴan sanda da sauran manyan jami’an ƴan sanda a jihar wanda aka yi da safiyar yau Litinin.